Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa: Shugaban Amurka, Donald Trump ya nemi Najeriya ta amince ta karbi masu laifi ‘yan kasar Venezuela zuwa Najeriya saboda kasarsu taki karbarsu saidai shugaba Tinubu yaki amincewa

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Kasar Amurka ta nemi Najeriya ta karbi ‘yan kasar Venezuela masu laifi da take son mayarwa kasarsu ta Asali amma kasar tasu ta ki amincewa.

Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Yusuf Tuggar yace ba zai yiyu Najeriya na da nata matsalar ba ta kuma dauko wata matsalar ta dorawa kanta.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne ya zo da wannan tsarin inda yake mayar da masu laifi zuwa kasashen su na Asali.

Saidai wasu kasashen na kin karbar masu laifin to idan aka samu irin wannan shine sai Trump ya nemi wata kasar wadda zata karbi masu laifin.

Karanta Wannan  Yawaitar rashin Aure na karuwa ne saboda mata suna yadda maza na Aikata Alfasha dasu>>Inji Dan majalisar jihar Nasarawa High Chief Otaru Douglas

Yayi irin hakan a baya inda ya aika ‘yan kasar Mexico, Cuba, da Venezuela da sauran wasu kasashe 5 zuwa kasar Sudan ta kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *