
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin kara kudin wutar Lantarki a Najeriya.
Rahoton yace Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a wajan wani taro a Abuja.
Yace za’a kara farashin kudin wutar lantarkin ne saboda dakatar da hauhawar da bashin da bangaren wutar ke fama dashi ke yi.
Naira Tiriliyan 4 ne ake bin bangaren wutar bashi.
Wannan magana tasa tana nufin, za’a dakatar da biyan kudin tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ke yi.
Hakan zai kara tsadar kudin wutar Lantarkin da ‘yan Najeriya ke biya.