Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwar kungiyar gamayyar ‘yan Adawa me suna AGOBI 27 sun nemi Atiku ya hakura ya barwa Peter Obi takarar shugaban kasa a 2027

Wata sabuwar kungiya me suna AGOBI 27 wadda gamayyar ‘yan adawa daga jam’iyyun (SDMA), da ADC da wasu kungiyoyin fafutuka suka kafa, ta roki tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya hakura da takarar shugaban kasa a 2027 ya barwa Peter Obi.

Kungiyar tace idan Atiku ya yadda da hakan, babu yanda Tinubu zai iya sake cin zabe a 2027.

Tace amma idan aka kasa samun wannan matsaya, lallai Tinubu ne zai sake cin zabe dan kuwa ya shirya hakan tsaf.

Kungiyar tace Atiku idan ya yadda da wannan kira, zai kasance wanda za’a rika tunawa dashi a tarihin Najeriya a matsayin wanda ya sadaukar da son ransa dan Najeriya ta ci gaba.

Karanta Wannan  Mun warware matsalolin aure aƙalla 600 a shekara ɗaya - HISBAH

Amma idan yace ba haka ba, ya bar Tinubu ya sake cin zabe, zai kasance wanda za’a rika tunawa a matsayin wanda ya biyewa son zuciyarsa maimakon ci gaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *