Tuesday, May 13
Shadow

Watanni 15 bayan fara biniken Tsaffin Ministocin jin kai, Sadiya Umar Farouk da Betta Edu har yanzu EFCC bata fitar da sakamakon binciken ba

A tsawon watanni 15 da suka gabata, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) bata fitar da cikakken rahoton binciken zargin almundahana da suka shafi tsofaffin Ministocin Harkokin Jinƙai, Gudanar da Bala’o’i da Ci gaban Zamantakewa — Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu.

Binciken, wanda ya kuma shafi tsohuwar Shugabar Hukumar Tsarin Tallafin Jama’a ta Ƙasa (NSIPA), Halima Shehu, da wani ɗan kwangila mai suna James Okwete, ya ci gaba da gudana a karkashin jagorancin EFCC, duk da dogon lokaci da ya wuce tun fara shari’ar.

Rahotanni sun nuna cewa, sama da naira biliyan 30 (N30bn) ne aka gano an dawo da su daga asusun bankuna kusan 50 da aka alakanta da ma’aikatar lokacin da Edu da Sadiya ke rike da madafun iko, bayan haɗin guiwa tsakanin EFCC da Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Nasaba da Cin Hanci (ICPC).

Karanta Wannan  Ka Yi Gaggawar Janye Kalamanka Kan Dokar Haraji Domin Zai Tada Hankulan 'Yan Kasa, Umarnin Fadar Shugaban Kasa Ga Gwamnan Bauchi

Yadda Rikici Ya Kunno Kai

Matsala ta fara fitowa fili ne bayan wani takardar memo ta bayyana a kafafen sada zumunta, inda aka bayyana cewa Betta Edu ta bukaci Akanta Janar na ƙasa a lokacin, Oluwatoyin Madein, da ta canja wurin naira miliyan 585 zuwa wani asusun kudi na mutum daya mai suna Oniyelu Bridget.

Ma’aikatar ta kare kanta da cewa Oniyelu Bridget ita ce ke matsayin Akanta na Ayyuka na shirin bayar da tallafi ga gungun marasa galihu.

Daga baya kuma, wasu takardu sun bayyana inda aka danganta Betta Edu da bayar da amincewa ta kasashen waje har da kudin jirgin zuwa Jihar Kogi — alhali jihar ba ta da filin jirgin sama.

Karanta Wannan  Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Sakamakon wadannan zarge-zarge, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Betta Edu daga mukaminta a ranar 8 ga Janairu, 2024.

Kwana bakwai kafin dakatar da Edu, an dakatar da Halima Shehu daga matsayin Shugabar Hukumar NSIPA bisa zargin karkatar da makudan kudade, inda Betta Edu ta bayyana cewa biliyoyin naira sun bace a karkashin jagorancinta.

Daga bisani, EFCC ta cafke Halima Shehu kuma ta yi mata tambayoyi dangane da zargin sauya wurin ajiyar naira biliyan 44 daga asusun NSIPA zuwa wasu asusun kamfanoni da na mutane cikin kwanaki hudu na watan Disamba 2023.

EFCC ta kuma gayyaci tsohuwar Ministar Jinƙai, Sadiya Umar-Farouq, domin amsa tambayoyi kan yadda aka tafiyar da naira biliyan 37.1 na kudaden tallafin jinƙai lokacin da take kan madafun iko.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu zai gabatar wa majalisa kudirin dokar kwarmata bayanai ba da jimawa ba - Ministan kudi Wale Edun

Copy KBC Hausa News
ABS Hausa News Nig

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *