Wednesday, May 28
Shadow

Wike da Gwamnonin PDP sun cimma matsaya kan makomar jam’iyyar

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike da Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun cimma matsaya kan makomar jam’iyyar.

Sun gana ne a Legas inda suka yadda da ci gaba da hadin kan jam’iyyar a ayin da ake fuskantar zaben shekarar 2027.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya wakilci gwamnonin PDP din a ganawar.

Wata Majiya tace an tattauna ne akan warware rikice-rikicen cikin jam’iyyar da suka hada da Rikicin jihar Rivers da na kudu maso kudu da kuma hedikwatar jam’iyyar da sauransu.

Tun bayan zaben shekarar 2023, jam’iyyar PDP ta fada cikin matsala.

Karanta Wannan  Yadda Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umarah Ya Gaisa Da Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima A Fadar Shugaban Kasa, Yau Laraba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *