
Kungiyar gwamnonin Najeriya tace ba zata yi magana akan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ba.
Daraktan Kungiyar, Abdulateef Shittu ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan da aka saka shi gaba kan cewa me zasu ce game da lamarin.
Yace suna ta samun sakonni daga bangarori daban-daban na cewa su yi magana ko su dauki mataki.
Saidai yace wannan abu ne wanda ba zai yiyu ba, ya kara da cewa, ya kamata mutane su fahimci cewa, kungiyarsu na da gwamnoni daga jam’iyyu daban-daban masu ra’ayin siyasa daban-daban.
Yace yawanci abinda suke magana akai abune wanda ya shafi al’umma gaba daya irin su Ilimi, Haraji, Kiwon Lafiya da sauransu.
Yace wannan maganar kuma akwak wadanda zasu yi magana akai wanda ba sai sun saka baki ba.