
Gwamnonin jam’iyyar APC sun baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar mayar da hankali wajan yaki da Talauci.
Sun bayyana hakane a wata sanarwa da suka fitar ta bayan taron da suka yi a garin Benin City na jihar Edo.
Shugaban kungiyar gwamnonin ta APC, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya bayyana hakan a jawabin da ya karanto.
Gwamnonin sun goyi bayan tayar da komadar tattalin arziki da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke yi bisa hadin gwiwarsu.
Gwamnonin sun bayyana jin dadin hadakar aiki da ake samu tsakaninsu da gwamnatin tarayya inda suka ce ana samun ci gaba.
Saidai sun ce ya kamata a fadada zuba jari a bangaren samar da abinci, samar da ayyukan yi, da kawar da talauci da karfafa masu kananan masana’anu, da bayar da tallafi.