Thursday, May 8
Shadow

Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam’iyyar NNPP

Wanda ya kirkiro jam’iyyar NNPP, Boniface Aniebonam ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yi koyi da halin Marigayi Fafaroma Francis na son Talakawa.

Ya bayyana hakane a sakonsa na ta’aziyyar fafaroman inda yace babu ta yanda za’a yi a ci gaba da barin wagegen gibin dake tsakanin Talakawa da masu kudi yana kara karuwa amma ace ana son zaman Lafiya.

Yace dolene Gwamnati ta mayar da hankali wajan yaki da Talauci kuma hakan ba aikin gwamnati ne kadai ba hadda masu hannu da shuni.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda mutane ke guduwa daga karamar hukumar Ryom ta jihar Filato dan fargabar kai hàri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *