Friday, December 5
Shadow

Ya kamata ‘yan Najeriya su rima godewa kokarin da muke domin ita matsalar tsaro ba’a magance ta a rana daya>>Inji Me baiwa shugaban kasa shawara kan matsalar tsaro, Nuhu Ribadu

Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu yayi kira ga ‘yan Najeriya da su rika godewa gwamnati kan kokarin da take dan magance matsalar.

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakanne a wata ganawa da yayi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar Benue a ziyarar da ya kai jihar.

Yace idana aka kalli kasashe irin su Sudan zaka ga basu da gwamnati, hakanan kasashe irin su Afghanistan inda yace ya taba yin aiki a can suma wadanda Duniya ta taru dan ta yakesu sune a yanzu suke mulkar kasar.

Yace kasashe Irin su Burkina Faso da Nijar da Mali yanzu sojoji ne ke mulki yace dan haka matsalar tsaro ba matsala bace da za’a ce a magance ta a rana daya.

Karanta Wannan  Karyace:Fubara ya mayarwa da shugaba Tinubu martani bayan da yace bai tabuka komai ba yayin da aka kaiwa Bututun man fetur din Najeriya hari

Yace ya kamata ‘yan Najeriya su rika godiya su san cewa akwai wadanda ke aiki tukuru dan samar da tsaro a kasarnan.

Yace a yanzu wadannan ‘yan ta’adda babu wani guri da suke rike dashi a kasarnan, yace an samu ci gaba amma dai ba’a samu abinda ake so ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *