
Tsohon Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Adamu Garba ya bayyana cewa ya kamata ‘yan Najeriya su yi na’am da zuwan Amurka Najeriya dan ta magance mana matsalar tsaro.
Yace Amurkar zata yaki ‘Yan ta’adda dake Khashe mutane da kuma ‘yan siyasa masu sace kudaden da aka ware dan magance matsalar tsaro.
Ya kara da cewa, idan mutum baya cikin daya daga cikin biyun nan to bashi da matsala da kasar Amurka.
Hakan ya zowa mutane da mamaki musamman lura da cewa, Adamu Garba dan Arewa ne inda ‘yan Arewa da dama suka nuna rashin amincewa da wannan mataki na kasar Amurka.