Tuesday, May 20
Shadow

Yadda ‘yan tà’àddà suka kàshè sojoji suka kwashe màkàmài a sansanin soji a Borno, Sojojin dai sun tsere yayin da màhàràn suka afkawa sansanin nasu, saidai da gari ya waye sun koma, Kalli bidiyon Yanda sojojij ke kuka, da hotunan gawarwakin wadanda aka kashe birjik a kasa

Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno.

Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin.

Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “ISWÀP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda runduna ta 24 take.

Karanta Wannan  Ji yanda ta kaya tsakanin Shugaba Tinubu da Peter Obi a haduwar da suka yi a wajan rantsar da Paparoma

“’Yan ta’addan sun ƙona tankokin yaƙi kuma sun kwashi makamai daga sansanin sojin,” in ji shi.

Wannan daya daga cikin sojojin da aka kashe ne wanda tuni aka binne gawarsa.

Wani mazaunin Marte, gari mai nisan kilomita 38 daga Dikwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Dikwa, ya ce sun ji karar harbe-harben kuma daga bisani suka ga jirgin soji yana shawagi.

Ya ce, “mun samu labarin cewa an tura ƙarin jami’an tsaro kuma an ƙwato sansanin sojin, amma ’yan ta’addan sun sun sace makamai kuma sun koma motoci da rumbun makaman sojin da ke wurin.”

Ya ci gaba da cewa, “abin takaici mayaƙan sun tsare mata da ƙananan yara da dama a Sabon Marte, amma wasu da dama sun samu tserewa zuwa Dikwa domin tseratar da rayuwarsu.

Karanta Wannan  Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

“Ba a daɗe ba da ’yan ƙungiyar suka kai hari a Malam Fatori, inda suka kashe sojoji 21 da wani daga cikin kwamdojinmu.”

Daga watan Janairu zuwa yanzu an kai wa sansanonin soji da dama hare-hare a yankin Tafkin Chadi da kuma Dutsen Mandara da ke Dajin Sambisa a jihohin Borno da Yobe.

Kalli Bidiyon anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *