
‘Yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliba a jami’ar jihar Zamfara, Zarah Abubakar Shehu sun kasheta duk da karbar kudin fansa.
An sace tane tare da ‘yan uwanta biyu a ranar Nov. 3, 2024 inda suka nemi Naira Miliyan 35 a matsayin kudin fansa, saidai daga baya an koma Miliyan 10 bayan tattaunawa.
Saidai bayan da aka kai kudin fansar sun rike Zarah inda suka ce sai an sake kai musu mashina 4 da Engine oil.
Saidai bayan da aka kai musu, sunce Zahra ta rasu har sun binneta.