Friday, January 16
Shadow

‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hàrì a jihar Arewa

‘Yan Bindiga akalla 10 sun kai mummunan hari wani kauye me suna Chito dake karamar hukumar Ukum ta jihar Benue ranar Asabar.

Maharan sun kai harinne da misalin karfe 2:26 am inda suka shafe awanni 2 da mintuna 30 suna aikata masha’a.

Ance sun daki mutane da dama sannan suka saci kayan sawa da abinci da sauransu.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Dr. Isaac H. Mamkaa wanda malamine a kwalejin ilimi ta Katsina Ala ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ‘yan Bindigar sun ce zasu sake komawa su kai musu hari garin.

Karanta Wannan  Hotunan kananan yara da nake gani suna wahala a Gàzà akwai ban tausai, ina kira gareka da a kawo karshen wannan yàkì>>Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yiwa Benjamin Netanyahu magana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *