
Da yawan ‘yan fafutuka na jihohin yarbawa sun nemi da a kama tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a hukuntashi.
Wasu daga cikinsu sun ce a zamanin mulkinsa ya azabtar dasu da iyalansu ya jefa rayuwarsu cikin rashin tabbas.
A zamanin mulkin tsohon shugaban kasar da ya faru a tsakanin shekarun 1985 zuwa 1993 an gudanar da zaben Abiola wanda janar Babangida ya soke.
Wannan ya jawo hargitsi a wancan lokacin wanda har sai da aka kashe mutane akalla 100, kamar yanda rahotanni suka bayyana.
An kuma kama mutane da yawa saboda fitowa zanga-zanga musamman dan nuna rashin amincewa da soke zaben, daga cikin wadanda aka kama akwai Chief Gani Fawehinmi, Alao-Aka-Bashorun, Femi Falana, SAN, Femi Aborisade, Debo Adeniran, Kunle Ajibade.
Dan hakane suka hada baki suka ce bai cancanci yabo ba, kuma bai cancanci taron da aka yi akansa aka karramashi ba dan kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa.
Sun bayyana cewa, kawai dan IBB ya amince da laifukan da ya aikata hakan baya nufin a kyaleshi shikenan yaci banza ba.