Tuesday, January 7
Shadow

‘Yan kasuwar Man fetur sun baiwa gwamnatin tarayya shawarar sayar da matatun man fetur

‘Yan kasuwar Man fetur karkashin kungiyar,Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria sun baiwa Gwamnatin tarayya shawarar sayar da matatun man fetur mallakar Gwamnati.

Sun ce sayar da matatun zai taimaka wajan kara gasa a masana’antar ta man fetur.

Sun nemi Gwamnati data sayar da matatun man fetur na Warri da Kaduna.

Sun kuma baiwa gwamnantin shawarar zuba hannun jari a kasuwar gas ta CNG inda suka kuma nemi data tallafawa ‘yan kasuwa 10,000 da cire tallafin man fetur ya durkusar dasu da Naira Biliyan 100 dan su tsaya da kafafunsu.

Sanarwar wadda ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Dr Billy Gillis-Harry ta bayyana cewa sayar da matatun man zai rage yawan kudin da Gwamnati ke kashewa.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴáɲ Biɲdiĝa Na Cigaba Da Rąɲtayawa A Na Káre Daga Maboyar Su Tun Bayaɲ Zuwaɲ Ministan Tsaro Jihar Sokoto Bisa Umarnin Shugaban Kasa Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *