Kungiyar masu dillancin man fetur a karkashin PETROAN ta bayyana cewa, tana nan kan bakanta na man fetur din da zata shigo dashi daga kasar waje ya fi na matatar Dangote sauki.
Me magana da yawun kungiyar, Dr. Joseph Obele ya bayyana cewa dolene a bar kowa yayi kasuwancinsa ba tare da katsalandan ba tunda dai gwamnati tace ta cire hannunta daga harkar.
Kungiyar tace ta kammala shirin ta tsaf dan shigo da man fetur cikin kasarnan kamin watan Disamba.
Kungiyar ta kuma musanta ikirarin da Dangote yayi cewa, suna shirin shigo da man fetur gurbataccene tace wana kawai soki burutsu ne irin na Dangote wanda ya saba yi dan kawai a barshi shi kadai ya rika siyar da man fetur din.