
‘Yan Kudu, Musamman Inyamurai na bayyana cewa, kalaman Rashin kyautawa da me magana da yawun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Bayo Onanuga yayi akan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari tun kamin a binneshi da sanin Tinubu yayi su.
Bayo Onanuga a jiya, Kamin a binne Buhari ya yi martani kan wani Bidiyon yakin neman zaben Buhari da yayi a Ibadan inda yace ga alama nan ga masu cewa Tinubu baiwa Buhari komai ba kokuma Kuri’un Buhari Miliyan 12 ne kawai suka sa yaci zabe.
Wannan kalamai san basu wa mutane dadi ba inda akai Caaa akan Bayo Onanuga aka ce ya jira a binne Burin mana kamin ma ya fara wannan magana.
Da yawa dai sun yi kiran Tinubu ya tsigeshi daga mukaminshi dan wataran zai iya jawo masa matsala.
Inyamurai da yawa sun ce da sanin Tinubu Bayo Onanuga yayi wannan kalamai.
Da surutu yayi yawa sosai, Bayo Onanuga ya goge kalaman nasa.