Friday, January 16
Shadow

‘Yan majalisar Wakilai 2 sun bar jam’iyyar PDP da Labour Party zuwa APC

‘Yan majalisar wakilai biyu, Peter Akpanke, da Paul Nnamchi sun bar jam’iyyunsu inda suka koma jam’iyyar APC.

Akpanke ya fito daga jihar Cross River ne kuma an zabeshi a karkashin jam’iyyar PDP amma yanzu ya bar jam’iyyar zuwa APC.

Shi kuwa Nnamchi ya fito daga jihar Enugu ne kuma an zabeshi a karkashin jam’iyyar Labour party ne amma yanzu ya koma jam’iyyar APC.

Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ya sanar da komawarsu APC a yayin zaman majalisar ranar Talata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Sheikh Dr. Ahmad Gumi ke daurawa dansa da ya gama NDA mukamin 2nd Lieutenant

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *