
Bankin African Export-Import Bank ya bayyana cewa, Najeriya na kashe Dala Biliyan $1.1 wajan neman magani da lafiya a kasashen waje duk shekara.
Bankin yace hakan ba karamin koma baya bane ga ci gaban harkar Lafiya a Najeriya.
Wakiliyar bankin, Mrs Oluranti Doherty ce ta bayyana hakan a Abuja a waja wani taro da aka yi ranar Alhamis.
Tace ci gaba da dogaro da neman lafiya a kasashen waje na dakile zuba jari a bangaren Lafiya a Najeriya inda tace kuma hakan na yiwa gaba dayan harkar tattalin arzikin kasar illa.