‘Yan Najeriya da yawa ne suka bayyana jin dadinsu da amfani da man fetur din matatar man fetur ta Dangote.
Da yawa da jaridar Punchng ta yi hira dasu sun ce sun ji dadin amfani da man fetur din na matatar man fetur ta Dangote saboda yana dadewa bai kone ba a mota idan aka kwatantashi da wanda suke amfani dashi a baya.
Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa, ta yi hadaka da gidajen sayar da man fetur na MRS dan ta rika sayarwa ‘yan Najeriya man fetur din da Rahusa.
Wasu daga cikin wadanda aka yi hira dasu sun ce gwamnati ta yaudaresu kan matatar man fetur din Dangote inda suka ce man da ake shigowa dashi bashi da inganci.