
Malamin Addinin Islama, Sheikh Saidu Aliyu Maikwano ya bayyana cewa,Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa dan Shi’a ne shiyasa ma yake cewa a yiwa kasar Iran addu’a a yayin fadansu da kasar Israyla.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga yana wa’azi.
Malamin yace ‘yan shi’a basu da maraba da Yahudawa inda yace ko Khumaini daya tashi yin gudun Hijira, maimakon ya je kasar Musulmai, sai ya tafi kasar Faransa.
A kuma bayyana cewa ‘yan shi’a basu da banbanci da Yahudawa.
Malamin dai yace Musulmi kwarai ba zaiwa kasar Iran Addu’a ba.