Monday, April 28
Shadow

‘Yan shi’a sun gargadi Gwwmnatin tarayya ta sakar musu mutanensu ko kuma su kai kara kotu

Kungiyar ‘yan uwa musulmi wanda aka fi sani da shi’a sun nemi a sakar musu mutanensu sama 60 da suka hada da kananan yara wanda suka ce zasu maka gwamnatin tarayya, da Hukumar sojoji da ta ‘yansanda a kotu idan ba’a sakar musu mutanensu ba.

Kungiyar ta kara da cewa, a ko da yaushe zata iya kai kara kotu muddin ba’a sakar mata da membobinta ba.

Kungiyar ta bayyana hakanne a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Ta kara da cewa, an kama membobin nata ne a wajan wata zanga-zangar lumana da suka gudanar kwanannan a Abuja.

Gamayyar Lauyoyin kungiyar da suka hada da Mr. Bala Dakum, da kuma Yusha’u Usman Dakum sunce kusan membobin kungiyar Shi’a 26 da suke wakilta ne aka kashe ranar March 28, 2025 bayan da suka fito zanga-zanga.

Karanta Wannan  Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Sunce ‘yan shi’ar na gudanar da zanga-zangar Lumana a daidai Banex Area, Wuse Il, Abuja sai suka ci karo da tawagar sojoji rike da makamai inda suka fara harbinsu da harsashi na gaske.

Sukace an kashe 26, sannan sama da 30 sun jikkata inda aka kama guda 274.

Sukace sojojin sun mika wadanda suka kama hannun ‘yansanda inda aka kaisu wani wulakantaccen waje ake tsare dasu.

Sukace daga cikin wadanda aka kama akwai kananan yara 60 wanda aka hadasu da manyan masu laifi kuma duk kokarin ganin an sakesu ya ci tura.

Sun kara da cewa membobin kungiyar da suke karewa ta shi’a a ko da yaushe suna gudanar da ayyukansu cikin lumana amma jami’an tsaro ne ke afka musu.

Karanta Wannan  Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Lauyoyin sun kara da cewa suna kira ga gwamnati da ta baiwa kungiyar shi’a damar gudanar da ayyukanta kamar yanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da ‘yancin yin addini ga kowa.

Sun kuma bayyana cewa suna son a saki duka wanda ake tsare dasu amma suna neman a fara gaggauta sakin kananan yara da wanda suka jikkata.

Sannan sun ce akwai gawarwakin wadanda aka kashe suma suna neman a saki gawarwakin dan yi musu jana’iza kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Sannan sunce idan ba’a sakesu ba, zasu kai kara kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *