Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Bindiga sun kwace iko da sansanin horas da soji na Nagwamase Military Cantonment dake karamar hukumar Kwantagora a jihar Naija.
Hakanan aun kuma kori mutanen kauyukan dake kusa da sansanin.
Majalisar jihar Naija ce ta bayyana hakan inda ta ti kira ga gwamnati data ta kawo karshen ayyukan ‘yan ta’addan.
Jimullar Kauyuka 23 ne dai ‘yan Bindigar suka kwace iko dasu.
Dan majalisar jihar dake wakiltar Kwantagora, Abdullahi Isah ne ya kai maganar zauren majalisar ranar Talata inda yace sansanin horas da sojin dake da girma wanda yake a cikin karamar hukumar Kwantagora har zuwa karamar hukumar Mariga a yanzu yana hannun ‘yan Bindigar.
Ya bayyana cewa kasancewar ‘yan Bindigar a cikin sansanin yana a matsayin wata barazanane ga jama’ar yankin inda yace ya kamata a kawar dasu.
Bayan doguwar muhawara akan lamarin, majalisar jihar ta amince da wannan mataki.