
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB ya bayar da labarin yanda ya hadu da matarsa Maryam a cikin littafin tarihin rayuwarsa.
Babbangida yace asalin sunan matarsa shine Maria Okogwu kamin daga baya ta musulunta ta koma Maryam.
yace sun dade suna abuta kamin ya aureta.
Yace babban dalilin da yasa yayi aure shine an taba harbinsa a kirji aka kwantar dashi a gadon Asibiti a Legas, anan ne yayi tunanin cewa ya kamata ace yayi aure.
Yace yana kan gadon Asibiti ya rika tunanin irin ‘yan matan da yake dasu da kuma da wacece cikinsu ya kamata ace yayi rayuwa a matsayin matarsa?
Yace anan tunanin Maryam ya fado masa, yace a lokacin tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon shima ya auri matarsa, Victoria inda abin ya kara karfafa masa gwiwa.
Yace yana warkewa sai ya tafi Kaduna ya samu Maryam ya nemi ta aureshi, yace amma addini na da matukar muhimmanci a wajansa dan hakane ma ya nemi ta musulunta, kuma ta yadda.
Saidai shima ya mata alkawarin ba zai kara aure ba, ita kadai zai zauna da ita musamman yanda yaga auren mata da yawa ya kawo rikici a gidaje da yawa.
An daura musu aure ranar September 6, 1969 kuma Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya 4, Aisha, Muhammad, Aminu, and Halima.
Babangida yace a shekarar 2009 ranar 27 ga watan Disamba, matarsa Maryam ta rasu kuma tun daga ranar rayuwarsa ta canja baya jin dadin rashinta.