Friday, December 5
Shadow

‘Yansanda a jihar Kano sun kama barayin a daidaita sahu su 4, an kwato keke Napep din sata 6 a hannunsu

Hukumar ‘yansandan jihar Kano sun kama barayin a daidaita su 4.

Kuma an kwato Keke Napep din sata guda 6 a hannunsu.

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Hussaini Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar yau Alhamis.

Yace a ranar 17 ga watan Yuni sun samu bayanan sirri kan wasu barayin adaidaita Namiji da mace, Auwal Mohammed, ‘m’, 30 wanda ke zaune a Hotoro, sai kuma Maryam Ibrahim, ‘f’, 25 wadda ‘yar jihar Bauchi ce.

Yace sun baiwa wani me adaidaita, Shu’aibu Aliyu kwaya suna kokarin kwace masa Keke Napep dinsa amma zuwan ‘yansanda yasa basu yi nasara ba.

Yace da bincike yayi tsanani an gano wani me suna Suleiman Lawal, wanda aka fi sani da Aljan da kuma Muhammad Tajuddeen, ‘m’, 32 wanda suke aiki tare dasu.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya nada dan tsohon shugaba kasa, IBB babban mukami

Yace an kwato a daidaita 6 daga hannunsu kuma za’a tabbatar an hukuntasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *