Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen binrin Abuja ta ce ta kama mutum 50 da take zargi da ɓallewa tare da sace murafe na kwatami a kan titunan birnin.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukan zumunta ta ce tsararren samame da ta kai ne ya ba ta nasarar kama mutanen, inda kuma dakarunta suka ƙwato murafe 25.
Birnin na Abuja ya daɗe yana fama da waɗannan sace-sace, inda ake yawan cire murafen da ke tsakiya ko gefen titi domin sayarwa.
“Bincike ya tabbatar cewa masu satar na aiki ne a matsayin wani gungu da ke sayar da murafen ga dillalan ƙarafa,” in ji sanarwar wadda ta lissafo sunayen mutum 50 ɗin.
Daga cikin abubuwan da ta ce ta ƙwace a hannun mutanen har da turakun lantarki masu amfani da hasken rana na gefen titi, da ababen hawa uku, da rodin gina gadodji, da sauran abubuwan da suke amfani da su wajen lalata kayan gwamnati.