Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Delta da ke kudancin ƙasar ta kama saurayi da budurwarsa bisa zargin haɗa baki domin damfarar iyayen yarinyar.
Da yake gabatar da matasan da aka ɓoye fuskokinsu a wani ofishin ‘yansanda, kakakin rundunar SP Bright Edafe ya ce matasan sun tsara cewa saurayin ya kira mahaifan budurwar ya ce ya sace ta kuma nemi kuɗin fansa.
Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama matasan ne bayan mahaifiyar budurwar ta kai musu rahoton sace ‘yar tata.
A cewarsa: “A ranar 30 ga watan Disamba Princess mai shekara 21 ta je gidan saurayinta Prince kuma ta ba shi shawarar cewa su haɗa baki don neman kuɗi a wajen iyayenta.
“Prince ya kira iyayen nata kuma ya ce musu ya yi garkuwa da ita, har ma ya nemi kuɗin fansa naira miliyan biyu.”
Matashiyar wadda ta yi magana daga baya a ofishin, ta ce sun yi niyyar su raba kuɗin ne a tsakaninsu.