
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya yadda akwai matsalar tsaro a Najeriya.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina.
Shugaban ya sha Alwashin yin amfani da dukkan kayan yaki na zamani da sauransu dan magance matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ya jadda cewa, idan ba’a magance matsalar tsaro ba, masu zuba jari ba zasu iya zuwa Najeriya ba.