
Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, an baza jami’an tsaro a yayin da ake shirin komawar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC.
A yau 12 ga watan Janairu ne dai ake tsammanin Gwamna Abba zai koma jam’iyyar APC.
Tuni tsohon shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar ta Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya koma Kanon daga Dubai dan halartar wannan taron.