Friday, December 12
Shadow

YANZU-YANZU: Gwamna Bago Ya Sanya Dokar Ta Baci A Garin Minna Biyo Bayan Rikìçe-Ŕikicen Ta Ta’ďdançi

Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar taƙaita zairga-zirgar baburan haya daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar sakamakon yawaitar rikicin ‘yan daba a birnin.

A cewar gwamnan, yanzu haka an takaita zirga-zirgar ‘yan acaɓa da babura masu ƙafa uku a wannan tsakanin.

Bago ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati yau Talata.

”Babu wanda zai sake ɗaukar kowane irin nau’i makami a garin Minna. Ina bai wa jami’an tsaro umarni, duk mutumin da kuka gani da makami ku ɗauke shi a matsayin ɗanfashi da makami.” in ji shi.

Karanta Wannan  Ina mamaki idan naga 'yan Siyasa na turuwa zuwa gidan Buhari, Buhari yawa 'yan Najeriya yaudarara da ba'a taba musu irinta ba>>Inji Buba Galadima

Ya bayyana cewa sabon matakin na da nufin daƙile matsalolin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a babban birnin jihar.

Ya kuma umurci hakimai da dagatai da masu unguwanni da su fara aikin tantance duk wasu baƙi da ke shiga yankunansu.

Ya kuma yi gargaɗin cewa za a ruguza duk wani gida da aka samu yana ɗauke da waɗanda ake zargi da aikata laifuka ko kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *