Thursday, May 22
Shadow

YANZU-YANZU: Matatar Man Fetur Ɗin Dangote Ta Sake Zaftare Farashin Man Fetur

YANZU-YANZU: Matatar Man Fetur Ɗin Dangote Ta Sake Zaftare Farashin Man Fetur.

Matatar sinadarai ta Dangote ta sake yin wani rangwame a kan tsohon farashin man fetur na Premium Motor Spirit wanda aka fi sani da man fetur kasa da Naira 835 da aka bayyana a bainar jama’a kan kowace lita.

Majiya mai tushe ta tabbatar a ranar Litinin din da ta gabata cewa matatar ta rage farashin ta zuwa Naira 825 ga kwastomominta, ta hanyar rangwamen Naira 10 bayan samun nasarar lodin kayayyakin a matatar.

Majiyoyin sun ce har yanzu ‘yan kasuwar suna biyan Naira 835 kan kowace lita na kayayyakin amma ana mayar da su Naira 10 bayan an kwashe su daga matatar.

Karanta Wannan  Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Daidaita farashin da aka yi a boye ya baiwa kwastomominsa da ‘yan kasuwa damar siyar da kayan a kan wani karamin kudi daga Naira 830 zuwa N835, wanda hakan ya zarta masu shigo da kaya da masu gidajen ajiya masu zaman kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *