Wednesday, January 15
Shadow

Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Rahotanni da muke samu daga gabas ta tsakiya na cewa, yaki ya barke tsakanin sojojin kasar Israela dana Misra/Egypt.

Lamarin ya farune a daidai Rafah, kaamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito.

A baya dai dama kasar ta Misra/Egypt ta gargadi Israela kada ta kai sojojinta yankin Rafah, saidai Israela ta yi kunnen uwar shegu da wannan gargadi indaa ta kai sojojin nata wajan.

Biyo bayan hakan itama Misra/Egypt ta jibge sojojinta a iyakarta ta Rafah.

To a yanzu dai yaki ya barke kamar yanda muke samun bayanai.

Rahoton yace sojojin Misra/Egypt ne suka fara budewa na Israela wuta inda suma na Israelan suka mayar da martani.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan Gawar Shugaban Kungiyar Hamass da Kasar Israela ta kashe ba kyan gani

Saidai zuwa yanzu dai babu rahoton jikkata ko kuma rasa rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *