Babbar Kotu tarayya dake da zama a Kano tace a fitar da Sarki Muhammad Sanusi II daga gidan Sarki dake Kofar Kudu
Kotun ta kuma ce a hukuncin da ta fitar yau, Talata, a mayar da Sarki Aminu Ado Bayero kan kujerar mulkinsa sannan a bashi dukkan abubuwan da doka ta bashi na sarauta.
Alkalin kotun, S.A Amobeda ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne dan amfanin al’ummar Kano da zaman lafiyar jihar.