Shugaban Ƙungiyar Ƙudirin samar da ‘Yancin Kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba.
A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60 ciki har da mazauna gida da ‘yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Da ya ke tattaunawa da jaridar The PUNCH a jiya Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Najeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala.
“Ba kwa jin muryar mu a tituna? Ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya.
“Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Najeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsayin Najeriya, babu matsala,” in ji shi.