Yarinyar nan mai shekara 14 da ƴansanda suka tuhuma da kashe abokin mijinta bayan zuba musu guba a abinci a jihar Jigawa ta amsa laifinta a gaban alƙali
Al’amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin 15 ga watan Disambar 2024 a ƙauyen Bakata da ke ƙaramar hukumar Kiyawan jihar Jigawa.
Yarinyar dai ta saka wa mijinta da abokansa guba a taliya, kuma nan da nan suka fita daga hayyacinsu, inda aka kai su asibitin garin Jahun inda a nan ne ɗaya daga cikin abokan mijin ya mutu.
Yarinyar ta amsa laifin saka gubar, sai dai kuma ta ce tsohon saurayinta wanda ɗanuwanta ne ya ba ta gubar domin ta saka wa mijin nata da abokansa a abinci.
Sai dai tsohon saurayin ya ce ba ya garin lokacin da yarinyar ta je garin. Yanzu haka yarinyar tana tsare a hannun ƴansanda inda shi kuma saurayin ke tsare a gidan yari. Alƙali ya ɗaga shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairun 2025.