Friday, December 5
Shadow

Yawan danyen man fetur din da Najeriya ke fitarwa ya ragu da kaso 4.37 cikin 100

Kungiyar kasashe masu arzikin Man Fetur, OPEC ta bayyana cewa, yawan danyen man fetur din da Najeriya ke fitarwa ya ragu a watan Maris.

Ta bayyana hakanne a cikin rahoton da ta fitar na watan Afrilu inda tace Najeriya ta samu ragin kaso 4.37 cikin 100 na yawan danyen man fetur din da take fitarwa.

Yawan danyen Man Fetur dun ya sauka daga ganga 1.465 da Najeriya ke fitarwa kullun zuwa Ganga 1.401.

Hakan dai yayi kasa da yawan man fetur din da kungiyar ta OPEC ke son kowace kasa dake cikin ta ta rika fitarwa na ganga Miliyan 1.5 a kullun.

An bayyana matsalolin rashin zuba hannun jari, da Tsaffin kayan aiki da kuma satar danyen man a matsayin abubuwan dake kawo tangarda wajan samun yawan danyen man fetur din da ake bukata.

Karanta Wannan  An Yi Zargin Kimanin Riyal Din Saudiyya 750,000, Kwatankwacin Sama Da Naira Miliyan Ɗari Uku, Wasu Masu Mulkin Nijeriya Suka Rinƙa Kama Ɗakunan Alfarma, (Presidential Suits) A Manyan Otel Ɗin Kusa Da Harami Dake Makka A Kwanakin Goman Karshen Watan Ramadan Da Ya Wuce, Cewar Alaramma Isma'il Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *