Wednesday, May 7
Shadow

Yawan kayan da kamfanoni ke sayarwa a Najeriya sun ragu saboda mutane basu da kudin saye

Rahotanni sun bayyana cewa yawan kayan da kamfanoni ke sayarwa a Najeriya sun ragu saboda mutane basu da kudin saye.

Kungiyar masu kamfanoni da masana’antu a Najeriya, MAN ne suka bayyana hakan.

Rahoton yace an samu karuwar kayan da ba’a sayarba zuwa kaso 87.5 wanda darajar kayan sun kai Naira Tiriliyan 2.14 a shekarar 2014.

Hakan ya nuna cewa yawan kayan da masana’antun basu siyarba ya karu idan aka kwatanta daga shekarar 2013 zuwa 2014.

Kayan da suka fi fama da wannn matsala sun hada dana abinci, da lemukan kwalba, da taba da kayan sawa da takalma da sauransu.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *