
Yawan ‘yan majalisar Jam’iyyar APC a majalisar tarayya ya karu bayan da ‘yan jam’iyyar Hamayya suka rika canja sheka kamar farin dango.
A yanzu yawan ‘yan majalisar dattijai na jam’iyyar APC sun karu zuwa 68 a yayin da yawan ‘yan majalisar wakilanta suka karu zuwa 207.
Hakan na zuwane yayin da majalisar ta 10 ta cika shekaru 2 da kafuwa.
Idan rahotannin dake cewa sanata Senator Neda Imasuen daga jihar Edo dan jam’iyyar Labour party zai canja sheka zuwa jam’iyyar APC suka tabbata, to yawan ‘yan majalisar Dattijai na jam’iyyar zai karu zuwa 69 kenan.
Hakanan yawan sanatocin APC din zasu karu idan Sanata Ahmed Wadada Aliyu daga jihar Nasarawa wanda ya bar jam’iyyar SDP ya koma jam’iyyar APC.
Ana zargin jam’iyyar APC da kokarin mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya.