Friday, December 26
Shadow

Yawanci ‘ya’yan fari a Najeriya ‘ya’yan shegu ne, ba ‘ya’yan halas bane>>Inji Binciken Smart DNA Nigeria

Babbar cibiyar binciken kwayoyin halitta na DNA me sunan Smart DNA Nigeria ta bayyana cewa yawan ma’aurata masu neman a musu binciken kwayoyin halitta da ‘ya’yansu na karuwa.

Cibiyar tace a shekarar 2025 an samu karuwar yin binciken kwayoyin halittar DNA da kaso 13.1 cikin 100.

Hakan na kunshene a cikin bayanin da kungiyar ta fitar wanda ya kunshi bayanan data tattara daga watan July 2024 zuwa June 2025.

Kafar tace wani abin damuwa shine yawanci musaman ‘ya’ya maza na fari da mata ke haifa ba mazajen ne iyayensu ba, daga waje suke shiga da cikin.

Rahoton yace kaso 65 na maza ‘yan fari ‘ya’yan shegu ne a Najeriya yayin da suma mata ‘ya’yan fari yawanci ba ‘ya’yan halas bane kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Karanta Wannan  Yanda me dafa babbar tukunyar Shinkafa ta Najeriya, Hilda Baci ta taka cikin tukunyar ta kuma wanke ta da Mofa ya jawo cece kuce

Saidai rahoton yace yawanci masu yin gwajin na DNA kaso 53 cikin 100 Yarbawa ne yayin da kaso 33 cikin 100 kuma Inyamurai ne inda kaso 1.2 na Hausawa ne kacal ke yin wannan Gwaji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *