
Bankin Duniya ya fitar da rahoto kan yanda ake raba tallafin rage radadin Talauci ga talakawa.
Bankin yace kaso 44 cikin 100 ne kacal na mutanen da aka ce ana baiwa tallafin ke samun sa.
Bankin yace kuma ko abincin da ake ciyar da dalibai ya kamata a karashi.
Hakan na zuwane bayan da ministan kudi Wale Edun yace sun raba naira 25,000 ga mutane Miliyan 8.5 inda ya kara da cewa akwai sauran mutane Miliyan 6.5 da zasu biya nan da karshen shekara.
Bankin Ya nuna damuwa kan yanda Najeriya ke kasancewa tana dogaro da kasashen waje wajan samun kudin da zata tallafawa Talakawanta.