
Jikan tsohon shugaban kasa, Marigayi Shehu Shagari me suna Nura Muhammad Mahe ya bayyana rashin jin dadin cewa irin karramawar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa Buhari bayan ya rasu, Buharin baiwa kakansu, Shehu Shagari irin hakan ba a lokacin da ya rasu yana kan shugaban kasa.
Mahe ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace kakansu, Tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari ya rasu a shekarar 2018 lokacin Buhari na shugaban kasa.
Yace Buhari bai je aka yi jana’izar Shagari dashi ba.
Yace sai daga baya ya aika tawagar gwamnatin tarayya wadda Boss Mustapha wanda ba musulmi a wancan lokacin suka musu gaisuwa.
Yace wannan wulakanci ne ga Shehu Shagari a matsayin shugaban kasar farko na mulkin Dimokradiyya