Thursday, February 5
Shadow

Yayin da Dalibai Kiristoci ke zargin an hanasu gona coci a jami’o’in Kashere, Gombe dana BUK, Kano, Shima wani dalibi musulmi yayi zargin cewa an hana Musulmai gina masallaci a jami’ar Jos, UniJos

A dazu ne hutudole ya kawo muku rahoton yanda wasu Kiristoci dalibai daga jami’o’in BUK, Kano da Kashere, Gombe inda suke zargin an hanasu gina coci a wadannan makarantu yayin da aka bar musulmai suka gina masallatai.

A martani ga wannan zargi shima wani dalibi musulmi yai zargin cewa an hana dalibai musulmai gina masallaci a jami’ar UNIJos, dake jihar Filato.

Yace duk da akwai masalacin da aka fara ginawa amma an hana a karasashi.

Sannan yayi zargin cewa an ma hana musulmai yin salla a masallacin da ba’a karasa ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda jami'an tsaro suka zagaye Nnamdy Khanu suna ta kokarin kwace abin magana daga hannunsa yayin da yake ta zhaghin Alkali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *