Thursday, February 26
Shadow

Yayin da Wutar Lantarki ta gagari Gwamnatin tarayya gyarawa, Shugaba Tinubu yayi sabuwar doka da ta baiwa Jihohi ragamar samar da wutar Lantarki a Najeriya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa sabon daftarin doka hannu wanda ya baiwa jihohin Najeriya damar samarwa da rarraba wutar Lantarki a jihohinsu.

Tun a shekarar 2024 daftarin dokar ya wuce amincewar ‘yan majalisa inda ake jiran shugaba Tinubu ya saka hannu amma bai saka ba sai a yau.

Masana sun ce hakan ya canja kula da wutar lantarki a Najeriya wanda a baya yake hannun Gwamnatin tarayya, a yanzu jihohi ne zasu rika samar da wutar.

Hakanan ana tsammanin wannan sabuwar dokar zata jawo masu zuba jari a harkar sannan zata karfafa gasa tsakanin jihohin wanda hakan zai inganta samar da wutar Lantarkin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon tallar A sake zaben shugaba Tinubu a 2027 da taurarin Kannywood ke yi ya jawo cece-kuce sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *