Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirin ƙara kuɗin kiran waya da na data, nan ba da jimawa ba.
Ministan sadarwar ƙasar, Bosun Tijani ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja.
Ya ce hukumar sadarwa ta ƙasar, NCC ce za ta tsara yadda ƙarin zai kasance.
Tijani ya ƙara da cewa, “Kafin mu zo da wannan shawara, sai da muka yi la’akari da abubuwa masu yawa na yadda hakan zai taimaka wajen gina ƙasarmu”.
“Wasu daga cikin abubuwan sun haɗa da tabbatar da inganta hanyoyin sadarwarmu da inganta kamfanoninmu na cikin gida da tabbatar da ɗorewar kamfanonin kansu”.
”Haka ma kamar yadda muke ganin hauhawar farashin kayayyaki a duniya, su ma kamfannonin sadarwar na fuskantar wannan matsala, don haka ba za mu bari su durƙushe ba, dole mu yi wani abu don tabbatar da ɗorewarsu”, in ji ministan.