Ana sa ran binne marigayi babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Taoreed Lagbaja ranar Juma’a a Abuja.
Yayansa da yake bi, Moshood Lagbaja, ne ya bayyana haka a garin Osogbo, jihar Osun a lokacin da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar St Charles Grammar School Osogbo, (SCOBA), ta kai wa iyalan ziyarar ta’aziyya.
Moshood ya ce hukumomin soji sun ce ba za su ba iyalan gawar marigayin ga, amma sun bayar da tabbacin cewa za a yi masa jana’iza da ta dace a Abuja, ranar Juma’a.
Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar rasuwar babban hafsan sojin na ƙasa ne da ta ce ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Kafin tabbatar da rasuwar, an fara raɗe-raɗin cewa babban hafsan ya rasu a sanadiyar cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje, inda masu yaɗa maganganun suka riƙa cewa an ɓoye rasuwar ne saboda masu rububin neman maye gurbinsa.