
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a sake zaɓar Shugaba Tinubu a 2027, musamman yanzu da jam’iyar APC ke ƙara samun yawan jihohi a ƙasar.
Yayin da yake maraba da takwaransa gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam’iyyar APC mai mulki cikin makonnan, Mista Okpebholo ya ce kasancewar a yanzu APC na iko da jihohi uku cikin shida na yankin kudu maso kudancin ƙasar yankin zai samu kulawar gwamnatin tarayya.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua ya fitar, gwamnan ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin jihohin Bayelsa da Rivers da kuma Akwa Ibom za su koma APC, wani abu da ya ce zai ƙara wa yankin tasiri a siyasance.
Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta lashe yankin kudu maso kudu a zaɓen 2027.
Mista Okpebholo ya kuma ce zai tabbatar da ingantuwar alaƙa tsakanin jiharsa da makwabtan jihohi domin cimma muradin jam’iiyarsa.