Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bijiro da sauye-sauyen “da suka zama dole” domin gina ƙasar.
Tun daga hawa mulkinsa wata 19 da suka gabata, an ga yadda Tinubu ya cire tallafin mai, ya sauya kasuwar canjin kuɗaɗen waje, ya gabatar da sabbin dokokin haraji, ya ƙaddamar da tallafin karatu, ya ƙara mafi ƙanƙantar albashi.
“Za mu ci gaba da bijiro da sauye-sauyen da suka zama dole domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa da yalwa a ƙasarmu,” in ji shi cikin saƙonsa na sabuwar shekara.
“Muna kan hanya mai kyau ta gina Najeriya wadda za ta kyautata wa kowa da kowa. Kada mu bari wasu ‘yan tsirari daga cikinmu da ke amfani da siyasa da addini da ƙabilanci su kawar da hankalinmu.”