Wednesday, January 8
Shadow

Za’a dauke wutar lantarki ta tsawon sati 2 a Abuja

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, ana tsammanin za’a dauke wutar lantarki a Abujan na tsawon makonni 2.

Kamfanin rarraba wutar na Abuja, AEDC ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar inda yace za’a fara samun matsalar ne daga ranar Litinin, 6 ga watan Janairu zuwa 21 ga watan.

Kamfanin yace hakan zai farune dalilin wani gyara da zasu yi.

Guraren da matsalar zata shafa sun hada da Lugbe, Airport Road, Kapwa, NNPC, Games Village, National Stadium, Eye Clinic, Indoor Complex, Christ Embassy Church, American International School, Spring Court, American Embassy Quarters, EFCC Headquarters, Coca Cola, Railway, da Federal Medical Centre (FMC), Jabi.

Karanta Wannan  Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda

Sai kuma Apo, Gudu, Gbazango, Kubwa, Bwari, Jahi, Jabi, Karu, Nyanya, Mararaba, Keffi.

A karshe kamfanin ya bayar da hakuri kan matsalar da hakan zata haifar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *