Saturday, March 15
Shadow

Za’a rage farashin kiran waya dana data daga kaso 50 zuwa kaso 35

Rahotannin da kafar hutudole ta samu na cewa, za’a rage farashin kudin kiran waya dana data daga kaso 50 da aka kara zuwa kaso 35.

Hakan ya bayyanane a cikin jawabin da shugaban kungiyar NLC ya fitar inda suke barazanar shiga yajin aiki idan ba’a yi wannan ragi ba.

Hutudole ya faimci cewa, an yi zama tsakanin Gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro inda aka cimma matsaya gane da karin kudin kiran waya dana data, maimakon kaso 50 cikin 100 da aka yi, yanzu zai koma kaso 35 cikin 100.

Kungiyar NLC tace idan ba’a tabbatar da wannan kari ba, zata tafi yajin aiki.

Karanta Wannan  An kama matashi da ya kkàshè Budurwarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *