Saturday, March 15
Shadow

Zaku yi Azumi cikin Mutunci da jin dadi saboda zamu tabbatar an samu tsayayyar wutar Lantarki>>Gwamnatin Tarayya ta baiwa Musulmai tabbaci

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa, musulmai zasu yi Azumi cikin mutunci da Jin dadi saboda zasu samar da tsayayyar wutar lantarki.

Ministan wutar, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Yace Yana sane da bukatar wutar lantarki da Musulmai masu azumi ke da musamman lokutan Sahur da Shan Ruwa da lokacin Taraweeh.

Yace dan haka zasu yi kokarin samar da tsayayyar wutar Lantarki a lokacin Azumin watan Ramadana dana har gaba dan musulmai su yi Azumi cikin jin dadi da Mutunci.

Ya bayar da shawarar cewa idan ya zamana ba’a amfani da wutar ko in za’a kwanta ko in za’a fita daga gida a rika kashe kayan wutar lantarki dan hakan zai taimaka matuka wajan ragewa tashoshin wutar Najeriya lodi.

Karanta Wannan  Ka Hakura da neman zama shugaban kasa, Allah be kaddaro maka zaka mulki Najeriya ba>>Wike ya gayawa Atiku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *